Wasanni-Wariya

Thierry Henry ya janye daga shafukan sada zumunta saboda kalaman wariya

Tsohon dan wasan Arsenal da Faransa Thierry Henry.
Tsohon dan wasan Arsenal da Faransa Thierry Henry. Sebastien ST-JEAN AFP/Archives

Tsohon dan wasan gaba na Arsenal da Faransa Thierry Henry ya sanar da janyewa daga ilahirin shafukan sada zumunta saboda tsanantar kalaman nuna wariya, da ya ce suna kokarin nakasa harkokin wasanni musamman kwallon kafa.

Talla

Henry mai shekaru 43 da ke cikin masu horar da tawagar kwallon kafar Faransa yanzu haka ya ce tsanantar matsalar nuna wariyar kan ‘yan wasa ta kai kololuwar da bai kamata a kawar da kai ba.

Tsohon dan wasan na Arsenal wanda ya dage kofin Firimiyar har 3 da Club din ko a makon jiya ya bayyana irin kalubalen wariyar da ya fuskanta yayin taka ledarsa, sai dai ya ce a wancan lokaci nasu da sauki domin kuwa a iya filin wasa ne su ke cin karo da matsalar, sabanin yanzu da ya ce matsalar na bin 'yan wasa har gadon barcinsu.

A cewar Henry wanda ya taka leda da Arsenal daga 1999 zuwa 2007 lokaci ya yi daya kamata a dauki matakin bai daya na shawo kan matsalar inda ya ce a nasa bangaren iyakar abin da zai iya kenan. 

Shima dai dan wasan gaba na Wales da ke taka leda a Tottenham ya ce a shirye ya ke ya kauracewa shafukansa na sada zumunta matukar aka kaddamar da gangamin hakan yayinda Wilfred Zaha na Crystal Palace ke cewa a kowacce rana cikin fargaba ya ke bude shafukansa na sada zumunta saboda tsoron kalaman na nuna wariya da ya san dole ne sai ya ci karo da su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.