Wasanni-Faransa

Faransa: Annobar Korona na barazana ga gasar Rolland Garros

Filin gasar kwallon Tennis ta French Open ko Roland Garros da ke birnin Paris a kasar Faransa.
Filin gasar kwallon Tennis ta French Open ko Roland Garros da ke birnin Paris a kasar Faransa. AP - Michel Euler

Shugaban tawagar kwallon tennis na Faransa Gilles Moretton bayyana fatan ba za a soke gudanar babbar gasar tennis a duniya ta Rolland Garros ba, saboda cigaba da ta’azzarar annobar Korona a kasar ta Faransa.

Talla

An dai tsara soma gasar ta Rolland Garros ne daga ranar 23 ga watan Mayu zuwa 6 ga watan Yuni, sai dai sake barkewar annobar Korona a Faransa dake karbar bakuncin gasar ya haifar da shakku kan yiwuwar gudanar ta.

Alkaluman baya bayan nan da ma’aikatar lafiyar Faransa ta wallafa sun nuna karuwar adadin mutanen da ke kamuwa da cutar Korona kullum a kasar zuwa akalla dubu 40, yayin da asibitoci suka yi cikar kwari a yankunan da cutar tafi kamari, ciki har da birnin Paris.

Tsakiyar filin wasan kwallon Tennis dake karbar bakuncin gasar Roland Garros a Paris, babban birnin kasar Faransa.
Tsakiyar filin wasan kwallon Tennis dake karbar bakuncin gasar Roland Garros a Paris, babban birnin kasar Faransa. AP - Michel Euler

A shekarar bara dai gasar tennis din ta Rolland Garros ta gudana ne a watannin Satumba da Oktoba, a maimakon Mayu da Yuni saboda annobar Korona, inda aka takaita yawan masu kallon kowane wasa da ya gudana a gasar zuwa dubu 1 kacal.

A jiya Laraba Shugaban faransa Emmanuel Macron ya sanar da matakin rufe ilahirin makarantun kasar daga mako mai kamawa, da kuma fadada dokar kullen dake aiki a birnin Paris da wasu yankunan da annobar ta Korona tayi kamari zuwa fadin kaar baki daya, domin dakile cutar da ke sake yaduwa cikin gaggawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.