Wasanni

Haaland na neman albashi mafi tsoka a tarihin gasar Firimiya

Fitaccen dan wasan Borussia Dortmund Erling Haaland.
Fitaccen dan wasan Borussia Dortmund Erling Haaland. AP - Martin Meissner

Fitaccen dan wasan gaba na kungiyar Borussia Dortmund, Erling Haaland ne neman zama dan wasa mai daukar albashi mafi tsoka a tarihin gasar Firimiya, bayan da rahotanni suka ce Haaland din ya nemi a rika biyanshi albashin fam dubu 600 duk mako, idan har ya kulla yarjejeniya da ko dai Manchester United ko kuma Chelsea.

Talla

Tuni dai Dortmund ta sanya farashin fam miliyan 130 kan matashin dan wasan nata mai shekaru 20, wanda ta kulla yarjejeniya da shi kan fam miliyan 20 kasa da watanni 16 da suka gabata.

Haaland dan kasar Norway da a yanzu haka Manchester United, City da kuma Chelsea ke neman kulla yarjejeniya da shi, ya ciwa Borussia Dortmund kwallaye 49 a jumillar wasanni 39 da ya buga musu tun bayan kulla yarjejeniya da shi.

Erling Haaland
Erling Haaland AP - Martin Meissner

Neman albashin fam dubu 600 da wakilin Haaland Mino Raiola yayi kamar yadda jaridar UK Sports ta ruwaito, na nufin cewa duk kungiyar da za ta kulla yarjejeniya da dan wasan, sai ta amince da biyansa akalla fam miliyan 300 jumilla a tsawon yarjejeniyar da za su rattaba hannu akai.

Yanzu haka dai Alexis Sanchez na kasar Chile ke rike da tarihin zama dan wasa mafi daukar albashi a gasar Firimiyar Ingila, bayan da Manchester United ta rika biyansa fam dubu 500 a duk mako.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.