Wasanni-Kwallon Kafa

Klopp ya roki tawagar Liverpool ta jajirce a wasanninta na Firimiya

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp. Peter Byrne POOL/AFP

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya roki tawagarsa da su jajirce wajen bayar da mamaki ta hanyar Karkare wasannin wannan kaka a ‘yan hudun saman Teburin Firimiya, dai dai lokacin da tawagar ke shirin komawa wasanninta bayan hutun tsakiyar kaka.

Talla

Yanzu haka dai wasanni 9 ya ragewa tawagar kuma ta na da tazarar maki 6 tsakaninta da Chelsea wato gurbin da ta ke hari, wanda ke nuna dole sai ta kaucewa kura-kuran da ta rika tafkawa a baya, matukar ta na bukatar samun tikiti a gasar cin kofin zakarun Turai na badi.

A gobe ne Liverpool za ta kara wasanta na 30 wato yayinda haduwarta da Arsenal wadda ita me ke ci gaba da samun koma baya a wannan kaka, ko da ya ke ta lallasa tawagar ta Jurgen a gaduwarsu ta karshe.

A cewar Klopp tawagar tasa za ta yi wasa ne don neman llahirin makin da ya rage, domin kuwa a yanzu basu da makin da za su yi asara kamar yadda suka faro a farkon kaka, ba kadai a gasar firimiya ba har da wasannin gasar zakarun Turai da suka ragewa Liverpool.

Babu dai bayanai kan lafiyar tarin ‘yan wasan tawagar da jinyarsu ta sanya mata barin maki da kuma samun koma baya daga mai kare kambu zuwa mai neman gurbin na hudu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.