Wasanni-Gasar Zakarun Turai

Ramos zai rasa karawar Real Madrid da Liverpool a gasar zakarun Turai

Mai tsaron baya na Real Madrid Sergio Ramos.
Mai tsaron baya na Real Madrid Sergio Ramos. AFP/Archivos

Mai tsaron bayan Real Madrid Sergio Ramos ba zai samu damar taka leda a karawar kungiyar ta sa karkashin wasannin cin kofin zakarun Turai da za ta kara da Liverpool ba, saboda raunin daya samu a kafarsa.

Talla

Sanarwar da Real Madrid ta fitar ta ce Ramos mai shekaru 35 ya samu raunin ne lokacin da ya ke dokawa kasarsa kwallo a wasannin neman gurbin shiga gasar EURO da suka gudana a takaitaccen hutun tsakiyar kaka da ‘yan wasa suka samu.

Real madrid na shirin karawa da Liverpool ne ranar 6 ga watan nan a zagayen farko na wasan gab dana kusa da karshe na cin kofin zakarun turai gabanin su sake haduwa a wasa na biyu ranar 14 ga watan.

Jaridun wasannin Spain sun ruwaito Ramos na cewa raunin ya matukar harzuka shi ganin yadda zai rasa haduwar ta cin kofin zakarun Turai da kuma wasan El Classico duk dai a cikin wannan watan wato haduwar Barcelona da Real Madrid.

A shekarar 2018 ne Real Madrid ta yi nasara kan Liverpool bayan zura mata kwallaye 3 da 1 baya ga targada hannun tauraron tawagar wato Mohamed Salah da Ramos ya yi a wancan lokaci dalilin da ya sanya wasu ke kallon haduwar a matsayin ta huce haushi duk da cewa Liverpool din ta yi nasarar dage kofin a 2019.

Dukkanin kungiyoyin biyu dai na fama da tarin majinyata wanda ya haddasa musu koma baya a wasanninsu na wannan kaka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.