Najeriya - Wasanni

NFF ta kaddamar da gasar kwallon yashi a Najeriya

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, Amaju Pinnick, yayin kaddamar da gasar Lig ta kwallon yashi ta Najeriya a birnin Legas.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, Amaju Pinnick, yayin kaddamar da gasar Lig ta kwallon yashi ta Najeriya a birnin Legas. © Twitter@thenff

Hukumar kula da kwallon kafa a Najeriya NFF ta kaddamar da gasar Lig ta kwallon yashi ta kasar, wato Nigeria ‘Beach Soccer League’ a turance.

Talla

Shugaban hukumar ta NFF Amaju Pinnick ne ya jagoranci kaddamar da soma sabuwar gasar kwallon yashin Najeriyar a jiya Lahadi.

Sabuwar gasar kuma za ta rika gudana ne a karkashin hadin gwiwar hukumar kwallon Najeriya, hukumar kwallon yashi ta duniya da kuma hukumar kula da kwallon yashin ta nahiyar Afrika.

A wasan farkon kwallon yashin da aka fafata na rukunin farko, kungiyar Kebbi BSC ta lallasa Badagary United da kwallaye 4-2.

A sauran wasannin da aka fafata Anambra BSC ta lallasa Kwara BSC da kwallaye 5-2. Yayin da a rukuni na 2, Igbogboa BSC ta doke takwarar ta Edo da 6-3, sai kuma Kada BSC da ta samu nasara kan Smart City da 6-4.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.