Wasanni - FIFA - UEFA

Guardiola ya caccaki FIFA da UEFA kan wahalar da ‘yan wasa

Mai horas da Manchester City Pep Guardiola
Mai horas da Manchester City Pep Guardiola AP - Rui Vieira

Kocin Machester City Pep Guardiola ya caccaki hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA da kuma ta Turai UEFA, wadanda ya zarga da tagayyara ‘yan wasa.

Talla

Guardiola ya ce hukumomin kwallon kafar na wahalar da ‘yan wasa ne ta hanyar tsara jadawalin buga wasanni masu yawa kusa da kusa ba tare da baiwa ‘yan wasan damar samun isasshen hutu ba.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da wani mai horaswa ke caccakar tsarin jadawalin wasannin hukumomin kwallon kafa na FIFA da UEFA ba, domin Jose Mourinho ya taba caccakar su kan batun a lokacin da yake horas da Manchester United, inda ya koka kan jumillar wasanni 67 da ‘yan wasansa za su buga a kakar wasa 1, ciki har da na gasar Europa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.