Wasanni - Gasar Zakarun Turai

Raina karfin kungiyar Real Madrid kuskure ne babba - Zidane

Mai horas da kungiyar Real Madrid Zinaden Zidane.
Mai horas da kungiyar Real Madrid Zinaden Zidane. AP - Francisco Seco

Mai horas da Real Madrid Zinaden Zidane, ya ce masu sharhi kan kwallon kafa da daman a tafka kuskuren yin wa kungiyar kallon raini, dangane da kokarin da take na lashe kofin gasar Zakarun Turai a bana, wanda zai zama shi ne karo na 14.

Talla

Zidane yayi gargadin kallon kadangare ake yiwa Kada ne gabannin zangon farko na wasan da za su fafata Liverpool a zagayen kwata final na gasar ta zakarun turai idan anjima, gasar da ya ce bai kamata a cire su daga cikin wadanda za su iya lashe ta ba.

Kakar wasa ta bana dai ba ta kancewa Real Madrid mai sauki ba, ko da yake sun kokarta wajen fuskantar kalubalen, abinda ya sa har yanzu suke da sauran fatan lashe ko dai kofin gasar La Liga ko kuma na zakarun Turai.

A La liga, tazarar dake tsakanin jagorar gasar Atletico Madrid da kuma Real ta ragu zuwa maki 3, bayan kayen da Atletico ta sha a wasan da Sevilla ta doke ta da 1-0.

A gasar Zakarun Turai kuma idan har kungiyar ta Real ta samu nasarar doke Liverpool, hakan na nufin za ta kara da ko dai Chelsea ko FC Porto a zagayen kusa da na karshe wato Semi Final.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.