Kwallon Kafa

Shin Liverpool za ta rama abin da Madrid ta yi mata?

Real Madrid ta lallasa Liverpool da kwallaye 3-1 a wasan karshe na gasar zakarun Turai a 2018.
Real Madrid ta lallasa Liverpool da kwallaye 3-1 a wasan karshe na gasar zakarun Turai a 2018. AFP/Paul ELLIS

Yau ne ake komawa fagen gasar cin kofin zakarun Turai matakin gab da na kusan karshe, inda  Real Madrid da Liverpool za su maimata irin haduwar da suka yi a wasan karshe na gasar shekaru uku da suka gabata, lokacin da Sergio Ramos ya balla kafadar Mohamed Salah, abin da ya tilasta wa dan wasan ficewa daga kan fili tare da share tsawon lokaci na zaman jinya.

Talla

Sai dai a wannan karo, Ramos ba zai  buga wasan na yau ba ballantana ya sake balla Salah sakamakon raunin da shi ma ke fama da shi yanzu haka.

A wancan lokacin dai, Real Madrid ce  ta dauki kofin gasar bayan ta lallasa Liverpool da kwallaye 3-1.

Magoya bayan Liverpool sun zura idanu don ganin gwanayensu sun rama abin da Madrid ta yi musu har ta haramta musu daukar kofin  gasar zakarun Turai a wancan lokacin.

Sai dai kocin Liverpool Jurgen Kloop ya ce, yaransa ba za su buga wasan na yau ba da sunan ramuwar gayya.

A bangare guda, za a barje gumi tsakanin Manchester City da Borussia Dortmund a Etihad duk dai a matakin na kwata fainal a gasar ta zakarun Turai.

Karawar kungiyoyin biyu na zuwa ne a daidai lokacin da kocin Manchester City Pep Guardiola ke jinjina wa dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland.

Haalanda mai shekaru 20, shi ke kan gaba wajen yawan kwallaye a gasar zakarun Turai ta wannan kaka, inda ya zura guda 10 a raga.

Yanzu haka ana ci gaba da alakanta Haaland da komawa Manchester City domin maye gurbin Sergio Aguero .

Sai dai Guardiola na ganin cewa, farashin da aka sanya kan dan wasan na euro miliyan 150 ya yi tsada, yana mai cewa, Manchester City ba za ta iya biyan abin da ya zarce euro milyan 100 kan dan wasa guda ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.