Wasanni - Gasar Zakarun Turai

Zakarun Turai: Real Madrid ta lallasa Liverpool, City ta doke Dortmund

Vinicius Junior (C) put Real Madrid in a commanding position against Liverpool in their quarter-final tie
Vinicius Junior (C) put Real Madrid in a commanding position against Liverpool in their quarter-final tie GABRIEL BOUYS AFP

Real Madrid ta samu nasarar doke Liverpool da kwallaye 3-1, yayin fafatawar da suka yi a zangon farko na wasan zagayen kwata final a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Talla

Real Madrid da ta karbi bakuncin Liverpool a Spain, ta samu nasarar ce daga ‘yan wasanta Vinicius Junior da ya ci 2 da kuma Marco Asensio. Yayin da ita Mohamed salah ya ci wa Liverpool kwallonta 1.

Just in time: Phil Foden (left)struck Manchester City's late winner against Borussia Dortmund
Just in time: Phil Foden (left)struck Manchester City's late winner against Borussia Dortmund Paul ELLIS AFP

A bangare guda kuma Manchester City ta samu nasarar doke Borussia Dortmund da 2-1, bayan da suma suka fafata zangon farko na zagayen kwata final a gasar zakarun turan.

Kevin De Bruyne da Phil Foden ne suka ciwa City kwallayen, yayin da Marco Reus ya ciwa Dortmund 1.

A gobe Laraba ne kuma za a fafata sauran wasannin zagayen kwata final din na gasar zakarun Turan tsakanin Bayern Munich da Paris Saint-Germain sai kuma FC Porto da Chelsea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.