Wasanni-Kwallon Kafa

Bayern Munich zata kara da PSG a gasar zakarun Turai

Kofin gasar zakarun Turai na UEFA
Kofin gasar zakarun Turai na UEFA Valentin FLAURAUD UEFA/AFP

Yau kungiyar Bayern Munich dake rike da kofin zakarun Turai zata kara da PSG a matakin kungiyoyi 8 na gasar zagaye na farko da zai gudana da misalin karfe 8 na dare.

Talla

Kungiyar ta Bayern zata shiga wannan karawar ce ba tare da gwarzon dan wasan ta Serge Gnabry ba saboda ciwon makogoron da yake fama da shi, abinda yasa ake ganin za’a maye gurbin sa da Leroy Sane.

Dan wasan Bayern Munich  Robert Lewandowski.
Dan wasan Bayern Munich Robert Lewandowski. Christof STACHE AFP

Daga bangaren PSG kuma yan wasa irin su Alessandro Florenzi da Marco Verratti zasu kauracewa wasan saboda harbuwa da cutar korona da suka yi.

A karawar da za’ayi yau Neymar da Kylian Mbappe zasu jagoran masu kai hari na kungiyar PSG, a daidai lokacin da manaja Mauricio Pochetino ke kokarin kawo karshen nasarorin da kungiyar Bayern ke samu ba tare da kaukautawa ba.

Babban abin fargabar da PSG ke da shi shine gamuwa da Robert Lewandowski wanda ya kware wajen sanin sirrin raga.

Ko yaya kuke kallon wannan wasan zai kaya? Muna dakon ra’ayoyin ku

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.