Wasanni-Brazil

Brazil ta janye daga shirin sauya sunan Maracana zuwa Rei Pele

Filin wasa na Maracana da ke birnin Rio de Janeiro a Brazil.
Filin wasa na Maracana da ke birnin Rio de Janeiro a Brazil. Mauro PIMENTEL AFP/Archives

Majalisar dokokin jihar Rio de Janeiro a Brazil ta janye kudirin sauya sunan katafaren filin wasan kasar na Maracana zuwa sunan tauraron kwallon kafar kasar Pele bayan da shirin ya janyo cece-kuce ya kuma gamu da kakkausar suka daga bangarori daban-daban.

Talla

Kakakin Majalisar Andre Ceciliano da ya gabatar da kudirin tun a wancan lokaci ya bukaci kadawa shirin kuri’a maimakon sanya masa hannu kai tsaye, wanda ya bayar da damar kada kuri’a a ranar 9 ga watan maris, aka kuma amince da sauya sunan zuwa Rei Pele don girmama zakaran kwallon wanda ya dage kofin Duniya sau 3.

Sai dai masu sukar matakin, sun zargi gwamnati da kawo batun sauya sunan na Maracana a dai dai lokacin da bai kamata ba maimakon daura damarar yaki da coronavirus da ke ci gaba da kashe rayuka.

A kalaman Ceciliano da ya gabatar da kudirin ya ce manufarsa shi ne kawai girmamawa da kuma yaba bajintar da Pele ya yiwa kasar a matakin kwallo amma Maracana za ta ci gaba da kasancewa Maracana ga al'ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.