Wasanni-Kwallon Kafa

FIFA ta fitar da jerin sunayen kasashe da matakin da suke da shi bisa kokarin su

 Gianni Infantino, Shugaban hukumar kwallon kafar Duniya
Gianni Infantino, Shugaban hukumar kwallon kafar Duniya FRANCK FIFE AFP/Archives

Hukumar Kwallon kafa ta duniya ta fitar da jerin sunayen kasashen duniya da matakin da suke da shi bisa kokarin su wajen murza kwallo na wannan wata, wanda ya nuna cewar Najeriya ce ke mataki na 32 a fadin duniya kuma mataki na 3 a fadin Afirka baki daya.

Talla

Wannan ya biyo bayan nasarorin da kungiyar Super Eagles ta samu a baya bayan nan da suka hada da doke Jamhuriyar Benin da ci 1-0 da kuma samun nasara kan Lesotho da ci 3-0.

 Gianni Infantino, Shugaban hukumar kwallon kafar Duniya
Gianni Infantino, Shugaban hukumar kwallon kafar Duniya Kurt SCHORRER FIFA/AFP

Wadannan nasarori sun nuna cewar Najeriya ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin Afirka da za’ayi a kasar Kamaru a wannan shekara.

Kasar Senegal ce kasar Afirka ta farko a jerin sunayen da FIFA ta fitar kuma itace ta 22 a duniya, sai Tunisia a matsayi na 2 a Afirka, kuma ta 26 a duniya.

A matakin duniya Belgium ke matsayi na farko sai Faransa a matsayi na biyu sannan Brazil a matsayi na 3.

Rahotan FIFA yace England na matsayi na 4, yayin da Portugal ke matsayi na 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.