Wasanni - Ingila

Europa: Wasan Arsenal da Slavia Prague ya bar baya da kura

Mai horas da kungiyar Arsenal Mikel Arteta
Mai horas da kungiyar Arsenal Mikel Arteta AP - Kirsty Wigglesworth

Tsohon dan wasan Arsenal Martin Keown ya gargadi kocin kungiyar Mikel Arteta da cewar yana cikin hadarin rasa aikinsa, biyo bayan wasan da Arsenal din ta tashi kunnen doki wato 1-1 tsakaninta da Slavia Prague ranar Alhamis a gasar cin kofin Europa.

Talla

Arsenal mai masaukin baki ce ta soma jefawa Slavia Prague kwallo ta hannun dan wasanta Nicolas Pepe, yayin da ya rage mintuna 4 a tashi daga wasan, sai dai jim kadan bayan samun nasarar, abokiyar hamayyar ta ta rama gabannin karkarewa.

Tashi kunnen dokin dai ya fusata magoya bayan Arsenal da dama, abinda ya sanya masana tamaula, ciki har da Martin Keown sharhin cewar ba shakka makomar aikin horas da kungiyar da Arteta ke yi zai fada cikin halin rashin tabbas, muddin lamurra suka ci gaba da tafiya ba daidai ba.

Yanzu haka dai Arsenal ce ta 10 a gasar Firimiyar bana da maki 42, tazarar 32 tsakaninta ta ta farko Manchester City mai maki 74.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.