Najeriya-Kwallon Kafa

Ahmed Musa na gab da komawa Kano Pillars

Ahmed Musa.
Ahmed Musa. PHILL MAGAKOE / AFP

Rahotanni daga Najeriya na cewa kungiyoyin Kano Pillars da Filato United na takarar daukar kaftin din tawagar Super Eagles, Ahmed Musa.

Talla

Komawar Musa Najeriya don ci gaba da murza tamaula, za ta dabbaka martabar gasar firimiyar kasar kamar yadda masharhanta  ke cewa.

Tun lokacin da ya raba gari da  Al Nasri ta Saudiya a cikin watan Oktoban bara,  Musa ke zaune ba tare da wata kungiya ba.

Dan wasan ya shaida wa manema labarai cewa, ya gana da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kuma Shehu Dikko, shugaban Hukumar Kula da Gasar Lig ta Najeriya game da yiwuwar komawarsa gasar ta firimiyar kasar.

Dan wasan ya taka leda a Ingila da Rasha da kuma Turkiya.

A wata hira da ya yi da RFI Hausa makwanni biyu da suka gabata, dan wasan ya shaida mana cewa, akwai yiwuwar ya koma Ingila don ci gaba da taka leda a gasar firimiyar kasar, kuma tuni tattaunawa ta yi nisa a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.