Wasanni - Italiya

Juventus na nazarin mikawa Everton 'yan wasa 4 kan Moise Kean

'Yan wasan kungiyar Juventus.
'Yan wasan kungiyar Juventus. © Reuters

Rahotanni daga birnin Turin na Italiya sun ce, kungiyar Juventus na nazarin yiwa Everton tayin mika mata ‘yan wasanta 4 dake cikin tawagarta ta farko, a matsayin musayar kulla yarjejeniya da Moise Kean, dan wasan kungiyar ta Everton.

Talla

Kean tsohon dan wasan gaba na Juventus ne a matakin karamar tawagar ‘yan wasan kungiyar kafin ya sauya sheka daga gasar Seria A zuwa Ingila kan euro miliyan 30.

A halin yanzu Kean mai shekaru 21, yana haskawa a kungiyar PSG ne a matsayin aro daga Everton, a karshen kakar nan kuma zai koma Ingila da Faransa, sai dai wasu majiyoyi sun ruwato cewar PSG na son mayar da yarjejeniyar ta da dan wasan ta dindindin.

A daidai wannan lokacin ne kuma, Juventus ta ke Nazari kan yiwa Everton tayin mika mata Adrien rabiot, Aaron Ramsey da kuma Demiral kamar yadda jaridar wasanni Tuttosport ta dake Italiya ta ruwaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.