Wasanni - Ingila

United ta lallasa Tottenham, Leeds ta doke City

Dan wasan Manchester United Bruno Fernandez yayin fafatawarsu da kungiyar Tottenham a gasar Firmiyar Ingila.
Dan wasan Manchester United Bruno Fernandez yayin fafatawarsu da kungiyar Tottenham a gasar Firmiyar Ingila. © Pool via REUTERS

Manchester United ta lallasa Tottenham da kwallaye 3-1 a wasan ranar Lahadi da suka fafata na gasar Firimiya.

Talla

Tottenham ce ta fara jefawa United kwallo ta hannun dan wasanta Son Heung-min, daga bisani kuma Fred, Edinson Cavani da Mason Greenwood su ciwa United na ta kwallayen 3.

A halin yanzu United ta rage tazarar maki 14 da Manchester City mai jagorantar gasar Firmiya ta ba ta, inda a yanzu ya koma 11, bayan da Cityn ta sha kaye a wasan da Leeds United ta doke ta da 2-1.

Har yanzu Manchester City ke jagorantar frimiya da maki 74, United da maki 63, s ai Leicester City da maki 56.

A can kasa ajin ‘yan dagaji kuma ta 18 da maki 26, West Brom na da maki 21 a matsayi na 19, sai ta karshe Sheffieled United mai maki 14.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.