Wasanni - Spain

Zidane ya kafa tarihin lallasa Barcelona sau 3 a jere cikin shekaru 42

Mai horas da Real Madrid Zinaden Zidane.
Mai horas da Real Madrid Zinaden Zidane. AP - Paul White

Mai horas da Real Madrid Zinaden Zidane, ya kafa tarihin zama kocin kungiyar na farko cikin shekaru 42 da ya jagoranci samun nasara kan babbar abokiyar hamayyarsu Barcelona sau uku a jere yayin wasannin El Clasico da suka fafata.

Talla

A ranar Asabar 10 ga watan Afrilu, Madrid ta samu nasara kan Barcelona da 2-1, nasarar da ta zama karo na 3 a jere tun a shekarar 1979.

Madrid da a yanzu ke matsayin ta biyu a teburin gasar La Liga da maki 66, ta jefawa Barcelona kwallaye 2 ne ta hannun ‘yan wasanta Karim Benzema da Toni Kroos, a yayin da Oscar Mingueza ya ciwa Barcelona 1.

Har yanzu Atletico Madrid ke jagorantar gasar La Liga da maki 67 duk da cewa ta yi kunnen doki 1-1 da Real Betis a wasan da suka yi jiya Lahadi, yayin da Barcelona ke matsayi na 3 da maki 65.

A karshen tebur Elche ce ta 18 da maki 26, deportivo Alaves ta 19 da maki 24 sai kuma Eibar ta karshe wato 20 da maki 23.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.