Zakarun Turai-wasanni

Lashe kofin zakarun Turai zai goge kuskuren da na yi a 2013- Gundogan

Dan wasan tsakiya na Manchester City Ilkay Gundogan.
Dan wasan tsakiya na Manchester City Ilkay Gundogan. Rui Vieira POOL/AFP

Dan wasan tsakiya na Manchester City Ilkay Gundogan ya ce yana fatan goge kuskure mafi girma da ya taba tafkawa a gasar cin kofin zakarun Turai, bayan rashin nasararsa a wasan karshe yayin taka ledarsa a karkashin Borussia Dortmund.

Talla

Gundogan wanda ke wannan batu gabanin karawarsu ta gobe Laraba da tsohuwar kungiyar tasa, ya ce kai Manchester City wasan karshe da kuma dage kofin kadai ne zai sassauta masa radadin da ke cikin zuciyarsa game da rashin dage kofin a 2013.

A shekarar 2013 ne Borussia Dortmund da taimakon Ilkay Gundogan karkashin jagorancin Jurgen Klopp da ke matsayin kocin tawagar a wancan lokaci, ta kai wasan karshe na cin kofin zakarun turai amma kuma ta yi rashin nasara a hannun Bayern Munich da kwallaye 2 da 1 a wasan wanda ya gudana a filin wasa na Wembley.

A cewar Gundogan rashin nasarar ta 2013 ita ce mafi munin shan kaye da ya taba damun zuciyarsa a fagen tamaula la’akari da irin jajircewar da tawagar ta yi a wancan lokaci wanda ya sa ya ke fatan kaiwa wasan karshe tare da dage kofin a yanzu.

Dan wasan wanda ke ci gaba da nuna bajinta, y ace dage kofin zakarun Turai a Manchester City yanzu zai zama babban tarihi la’akari da cewa yanzu haka cikin ‘yan wasan tawagar babu ko da dan wasa daya daya tab adage kofin inbanda mai horarwa Pep Guardiola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.