Wasanni-Kwallon Kafa

Magoya baya dubu 2 za su halarci wasan karshe na Carabao a Wembley

Filin wasa na Wembley da zai karbi bakoncin wasan karshe na gasar cin kofin kalubale wato Carabao.
Filin wasa na Wembley da zai karbi bakoncin wasan karshe na gasar cin kofin kalubale wato Carabao. Catherine Ivill POOL/AFP

Kungiyoyin kwallon kafa na Manchester City da Tottenham sun samu izinin baiwa magoya bayansu damar shiga kallon wasan karshe na cin kofin kalubale a filim wasa na Wembley.

Talla

Matakin wanda aka jima ana dambarwa kanshi don baiwa ‘yan kallo damar shiga filayen wasannin a Ingila karkashin dokokin dakile Coronavirus, sai a yau Talata ne hukumar kula da gasar ta baiwa kungiyoyin 2 damar sayar da tikitin kallon wasan wanda zai gudana ranar 25 ga watan nan.

Sanarwar da hukumar da ke kula da Carabao ta fitar ta nuna cewa kungiyoyin na Tottenham da Manchester City za su sayar da tikiti dubu 2 ga magoya bayansu amma bisa sharadin kare dokokin yaki da coronavirus.

Karkashin dokokin sayar da tikitin wanda zai zama irinsa na farko baza a sayarwa yaran da shekarunsu yayi kasa da 18 ba, haka zalika masu fama da rashin lafiya ko kuma mata masu masu ciki a wani yunkuri na dakile cutar.

Ka za lika gabanin baiwa ‘yan kallo masu tikiti shiga filin wasan na Wembley dole sai sun karbi gwajin corona haka zalika sai sun killace kansu na sa’o’I 24.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.