Wasanni - Italiya

Osimhen bai cancanci tsadar euro miliyan 70 ba - Giordano

Victor Osimhen dan wasan kungiyar Napoli dake gasar Seria A.
Victor Osimhen dan wasan kungiyar Napoli dake gasar Seria A. AP - Alessandro Garofalo

Tsohon dan wasan gaba na tawagar kwallon kafar kasar Italiya Bruno Giordano, ya ce tsohuwar kungiyarsa Napoli dake gasar Seria A ta tafka babban kuskure wajen kulla yarjejeniya Victor Osimhen dan wasan Najeriya da a baya ke taka leda a kungiyar Lille a Faransa.

Talla

A watan Satumban shekarar 2020 Napoli da kulla yarjejeniya da Osimhen mai shekaru 22 a yanzu, bayan biyan tsohuwarsa kungiyar ta Lille Euro miliyan 70, abinda ya sanya dan wasan zama mafi tsada a nahiyar Afrika.

Sai dai tsohon tauraron kwallon kasar Italiya Giordano yace Osimhen bai kai darajar kudaden da aka biya akansa ba, domin a cewarsa rashin cancantar hakan a bayyane take, idan aka kwatanta kwazo da kwarewar dan wasan Najeriya da takwarorinsa kamar Erling Haaland na kungiyar Borussia Dortmund.

Tsohon dan wasan kungiyar Napoli Bruno Giordano.
Tsohon dan wasan kungiyar Napoli Bruno Giordano. © Twitter/@sscnapoliES

Duk da sukar da yay ikan kudin da Napoli ta sanya wajen sayen Osimhen Giordano ya ce salon takar ledar dan wasan yana birge shi zalika ba shakka ya na baiwa kungiyar tasa. gudunmawa gaya.

Bruno Giordano ya haskawa kungiyar Napoli ne daga shekarar 1985 zuwa 1988, inda ya ci kwallaye 23 a wasanni 78.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.