Wasanni - Gasar Zakarun Turai

PSG da Chelsea sun tsallaka zagayen kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai

'Yan wasan PSG na murnar samun nasarar kaiwa zagayen kusa da na karshe a. gasar cin kofin zakarun Turai.
'Yan wasan PSG na murnar samun nasarar kaiwa zagayen kusa da na karshe a. gasar cin kofin zakarun Turai. FRANCK FIFE AFP

Kungiyoyin PSG da Chelsea sun samu nasarar tsallakawa zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai duk da cewa sun sha kaye a wasannin da suka fafata a yau a matakin kwata final zagaye na biyu.

Talla

Yayin wasannin na yau Talata, Bayern Munich ce ta samu nasara kan PSG da 1-0, said ai duk da haka taurarin Faransa ne suka samu nasarar kaiwa zagaye nag aba, la’akari da nasarar da suka samu kan Munich da kwallaye 3-2 a Jamus yayin fafatawar da suka a zagaye na farko.

Mai horas da Chelsea Thomasa Tuchel a tsakanin 'yan wasan kungiyar FC Porto.
Mai horas da Chelsea Thomasa Tuchel a tsakanin 'yan wasan kungiyar FC Porto. CRISTINA QUICLER AFP

Ita ma dai Chelsea rashin nasara tayi a hannun FC Porto da 1-0, amma duk da haka ta samu nasarar kaiwa zagayen gasar cin kofin zakarun Turan na gaba, la’akari da cewar a zagayen farko Chelsea ta doke Porto da 2-0.

A halin yanzu kungiyoyin biyu za su jira wadanda za su samu nasara a wasanni biyu da za a fafata ranar Laraba tsakanin Real Madrid da Liverpool sai kuma Borussia Dortmund da Manchester City.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.