Tawagar kwallon matan Amurka ta sha alwashin samun daidaito da maza

Tawagar 'yan wasan kwallon kafa na kasar Amurka mata, yayin murnar lashe gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ajin mata.
Tawagar 'yan wasan kwallon kafa na kasar Amurka mata, yayin murnar lashe gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ajin mata. AP - Darryl Dyck

Tawagar kwallon kafar mata ta Amurka ta sha alwashin cigaba da daukar matakan shari’a domin neman daidaita su da takwarorinsu maza wajen biyansu albashi da sauran alawus alawus.

Talla

Alwashin tawagar kwallon matan Amurka na zuwa bayan da alkalin wata babbar kotu a birnin Los Angeles ya yanke hukuncin daidaitasu da maza wajen samun hakkokin inganta basu kulawa da suka hada da masaukin otal-otal, adadin ma’aikata masu yi mudu hidima da kuma sufuri, amma banda bangaren biyan albashi, abinda ya sanya su soma shirin garzawa babbar kotun daukaka kara.

Tawagar kwallon matan Amurka da ta lashe gasar cin kofin duniya a shekarun 2015 da 2019  na neman gwamnatin Amurka ta biya ta diyyar. fiye da dala miliyan 66, saboda tauyewa matan hakkin daidaita su da maza da aka yi, said ai cikin watan May una shekarar bara, kotu ta yi watsi da bukatar matan.

A nata bangaren hukumar kwallon kafar Amurka ta bayyana fatan daidaitawa da ‘yan tawagar tamaular matan kasar kan korafin da suke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.