Wasanni - Gasar Zakarun Turai

City da Madrid sun shiga zagayen kusa da na karshen gasar Zakarun Turai

'Yan wasan Manchester City tare da kocinsu Pep Guardiola, yayin murnar kaiwa zagayen kusa da na karshen gasar Zakarun Turai.
'Yan wasan Manchester City tare da kocinsu Pep Guardiola, yayin murnar kaiwa zagayen kusa da na karshen gasar Zakarun Turai. WOLFGANG RATTAY POOL/AFP

Manchester City da Real Madrid sun samu nasarar kaiwa zagayen kusa da na karshe na gasar Zakarun Turai, bayan wasannin da suka fafata a daren ranar Laraba 14 ga watan Afrilu.

Talla

Yayin karawar ta da Borussia Dortmund, City ce ta samu nasara da 2-1, kamar dai yadda ta doke ta yayin fafatawar da suka a zangon farko na wasan zagayen kwata final.

Wannan ne karon farko da City ke kaiwa matakin kwata final a gasar cikin shekaru 3 da Guardiola ke jagoranci, kofin da saboda shi ne City ta dauki Guardiola a matsayin mai horarwa wanda ya kasha yuro miliyan 700 da ‘yan kai wajen kaiwa Etihad sabbin ‘yan wasa da nufin lashe kofin, amma har aynzu babu labari.

'Yan wasan Real Madrid da Liverpool yayin karawa a zango na biyu, na zagayen kwata final a. gasar cin kofin Zakarun Turai.
'Yan wasan Real Madrid da Liverpool yayin karawa a zango na biyu, na zagayen kwata final a. gasar cin kofin Zakarun Turai. GABRIEL BOUYS AFP/Archives

Ita kuwa Real Madrid ta samu nasarar ta ce bayan da tashi babu ci tsakaninta da Liverpool a filin wasa na Anfield dake Ingila. A zangon farko na fafatawar da suka yi Madrid ce ta doke Liverpool da 3-1 a Spain.

A halin yanzu, Real Madrid za ta kara ne da Chelsea, yayin da Manchester City za ta fafata da PSG a zagayen na kusa da na karshe wato Semi Final a turance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.