Wasanni

Liverpool na bukatar jajircewa a wasanta da Real Madrid - Klopp

Yanzu haka dai Real Madrid ke jagoranci bayan lallasa Liverpool da kwallaye 3 da 1 a haduwarsu ta farko.
Yanzu haka dai Real Madrid ke jagoranci bayan lallasa Liverpool da kwallaye 3 da 1 a haduwarsu ta farko. Clive Brunskill POOL/AFP/Archives

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce dolen ‘yan wasansa ne suyi wasa da dukkan karfinsu a karawarsu da Real Madrid yau Laraba, da nufin juya sakamakon karawar farko da suka sha kaye hannun tawagar ta Spain da kwallaye 3 da 1.

Talla

Matukar dai Liverpool na son kai labari a gasar ta cin kofin zakarun Turai, wajibinta ne ta zura akalla kwallaye 2 ba tare da barin Real Madrid ta zura ko da guda ba, lamarin da ke da matukar wahala, musamman ganin yadda Madrid din ke ruwan kwallaye a wasannin baya bayan nan.

A cewar Klopp sakamakon makon jiya na nuna tamkar Liverpool ta kammala ficewa daga gasar wanda ke matsayin abin da zai kara mata karsashi wajen jajircewa tare da kin karaya a karawar ta yau.

Klopp wanda ya kai Liverpool wasannin karshe na cin kofin gasar har sau 2 amma yayi rashin nasara a na farko hannun Real Madrid kana ya yi nasara a na biyu hannun Tottenham, ya ce matukar tawagarsa na bukatar kai labari dole ne ta yi amfani da salon tsaro na musamman don hana Madrid zura mata kwallo.

Manajan na Liverpool ya amsa cewa tabbas Real Madrid ta fisu karfi ta kowacce fuska amma hakan bazai sanyasu karaya a wasan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.