Wasanni-Kwallon Kafa

Liverpool da Borussia Dortmund sun fice daga gasar zakarun Turai

Wasan Liverpool da Real Madrid da aka tashi babu kwallo ko guda.
Wasan Liverpool da Real Madrid da aka tashi babu kwallo ko guda. Paul ELLIS AFP

Kungiyoyin kwallon kafa na Man City da Real Madrid sun bi sahun takwarorinsu na Chelsea da PSG wajen samun gurbi a wasannin gab da na karshe na cin kofin zakarun Turai yayin da suka yi waje da kungiyoyin Liverpool da Borussia Dortmond a karawar da ta gudana daren jiya.

Talla

Real Madrid ta yi nasarar fitar da Liverpool ba tare da zura kwallo ko guda daga bangaren kungiyoyin biyu a karawar ta jiya ba, amma da ya ke tana da rinjayen kwallaye 3 da 1 da ta zurawa tawagar ta Ingila a haduwar farko hakan ya bata damar tsallakawa mataki na gaba.

A bangare guda ita kuma City ta yi nasarar zurawa Dortmund kwallaye 2 da 1 wato kwatankwacin yadda suka tashi a haduwar farko wanda ya bata fifikon maki akanta.

Tun farko Borussia Dortmund ce ta fara zura kwallo a karawar ta hannun dan wasanta Bellingham a minti na 39 da fara wasa kafin tafiya hutun rabin lokaci amma kuma City ta farke bayan samun bugun fenariti kana ta kara kwallo ta biyu a minti na 75.

Yanzu haka Real Madrid za ta hadu da Chelsea ne yayinda Manchester City za ta hadu da PSG a zagayen gab da na karshe. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.