Wasanni-Kwallon Kafa

Mai yiwuwa a haramtawa Ibrahimovic buga wasanni tsawon shekaru 3

Zlatan Ibrahimovic, dan wasan kungiyar AC Milan dake gasar Seria A a Italiya.
Zlatan Ibrahimovic, dan wasan kungiyar AC Milan dake gasar Seria A a Italiya. AP - Antonio Calanni

Tauraron kungiyar AC Milan dan asalin kasar Sweden, Zlatan Ibrahimovic na fuskantar yiwuwar yanke masa hukuncin haramta mishi buga wasanni na tsawon shekaru 3, sakamakon bankado alakarsa da aka yi da wani kamfanin caca kan kwallon kafa dake tsibirin Malta.

Talla

Masu bincike sun gano cewar Ibrahimovic ya mallaki akalla kashi 10 na hannayen jarin kamfanin cacar kwallon kafa mai suna Bethard dake da ofisoshi a tsibirin na Malta, abinda ya sabawa dokokin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da kuma ta Turai UEFA.

Zlatan Ibrahimovic yayin kokarin jefa kwallo a ragar kungiyar Spezia.
Zlatan Ibrahimovic yayin kokarin jefa kwallo a ragar kungiyar Spezia. AP - Tano Pecoraro

Masu binciken sun kuma bankado cewar kamfanin dan wasan da ba a bayyana sunansa ba, shi ne na hudu wajen mallakar hannayen jari a kamfanin cacar kudaden kan kwallon kafa na Bethard dake Malta, wanda a shekarar 2019, ya samu ribar fam miliyan 25 bayan biyan kudaden haraji.

A karkashin dokokin hukumomin na UEFA da FIFA, muddin aka samu Ibrahimovic da laifi, zai fuskanci hukuncin haramta mishi wasanni tsawon shekaru 3, ko kuma biyan tara mai yawan gaske.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.