Wasanni

UEFA ta dakatar da dan wasan Slavia Prague kan kalaman wariya

Dan wasan Slavia Prague Ondrej Kudela yayin hatsaniyar da ta faru a wasansu da Rangers ta Scotland cikin watan Maris.
Dan wasan Slavia Prague Ondrej Kudela yayin hatsaniyar da ta faru a wasansu da Rangers ta Scotland cikin watan Maris. Ian MacNicol POOL/AFP/File

Hukumar UEFA ta dakatar da dan wasan Slavia Prague Ondrej Kudela daga doka wasanni 10 bayan samunsa da laifin furta kalaman wariya kan dan wasan tsakiya na Rangers Glen Kamara yayin karawarsu karkashin gasar Europa cikin watan maris din da ya gabata.

Talla

UEFA a hukuncin na ta bayan daukaka karar da Rangers ta yi kan batun ta kuma dakatar da shi kansa Kamara daga doka wasanni 3 haka zalika dan wasan gaba na tawagar Kemar Roofe daga doka wasanni 4 saboda hatsaniyar da ta faru a wasan, yayinda ta ci tarar kungiyar ta Slavia Prague yuro dubu 9 kan yadda ta gaza ladabtar da ‘yan wasanta.

Yayin wasan wanda Prague ta yi waje da Rangers a zagayen kungiyoyi 16 na gasar, sai da alkalin wasa ya fitar da Roofe baya ga Leon Balogun kan yadda hatsaniyar ta tsananta bayan kalaman wariyar da ya juye zuwa rikici tsakanin ‘yan wasan kungiyoyin biyu.

Sai dai Lauyan Kamara, Aamer Anwar ya ce babu gaskiya a ikirarin UEFA na cewa tana daukar matakan da suka kamata a yaki da nuna wariya cikin kwallo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.