Wasanni-Kwallon Kafa

Ahmed Musa zai samu horo a Kano Pillars-Rohr

Ahmed Musa
Ahmed Musa Ben STANSALL AFP/File

Kocin tawagar Super Eagles ta Najeriya Gernot Rohr ya yi amanna cewa, dan wasansa Ahmed Musa zai samu cikakken horo a gasar firimiyar kasar.

Talla

Kalamansa na zuwa ne bayan Kaften din na Super Eagles ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Kano Pillars don ci gaba da murza tamola.

Rohr ya ce, ya yi matukar farin ciki da dan wasan ya koma Kano Pillars saboda kungiyar na da kwarewa a cewarsa.

Kocin ya sha caccaka a lokacin da ya gayyaci Musa domin buga wa Najeriya wasanta da Benin da kuma Lesotho a gasar neman girbin shiga gasar kofin Afrika.

Kafin kulla yarjejeniya da Kano Pillars, dan wasan ya share tsawon watanni ya zaune ba tare da wata kungiya ba tun bayan da ya raba gari da Al-Nesyri ta Saudiya a cikin watan Oktoban bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.