Wasanni-Kwallon Kafa

Arsenal na da sauran aiki ja a gabanta - Arteta

Kocin Arsenal Mikel Arteta
Kocin Arsenal Mikel Arteta Tim Keeton POOL/AFP/Archives

Arsenal ta samu nasarar da kocinta  Mikel Arteta ya bayyana a matsayin mai muhimmanci, inda ta lallasa Slavia Prague da kwallaye 4-0, abin da ya bata damar samun gurbi a matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin Europa.

Talla

Arsenal ta nuna bajinta a yayin wasan na ranar Alhamis, inda a cikin minti shida ta zazzaga kwallaye uku a ragar Slavia Prague.

Nicolas Pepe da Alexendre Lacazette da kuma Bukayo Saka suka jefa kwallayen uku tsakanin minti 18 zuwa 24 da soma wasan, yayin da  Lacazette ya kara zura wata kwallon bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

A jumulce dai, Arsenal ta doke Slavia Prague da ci 5-1, idan aka hada da sakamakon wasansu na farko, inda suka tashi kunnen doki 1-1.

Yanzu haka Arsenal wadda ake yi wa kirari da The Gunners za ta hadu da Villareal ta Spain a matakin wasan dab na na karshe a ranar 29 ga wannan wat ana Afrilu.

Akwai aiki ja a gaban Arsenal saboda wajibi ne a gare ta ta lashe gasar Europa League muddin tana son samun gurbi a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai ta kaka mai zuwa, ganin cewa, har yanzu tana zaune a mataki na 9 a teburin gasar firimiyar Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.