Wasanni

Barcelona zata kara da Athletic Bilbao a gasar Copa Del Rey

Yan wasan Athletico Bilbao a fafatawa da kungiyar Barcalona
Yan wasan Athletico Bilbao a fafatawa da kungiyar Barcalona CRISTINA QUICLER AFP

Yau kungiyar Barcelona ta Spain zata kara da Athletic Bilbao a wasan karshe na cin kofin Copa Del Rey da zai gudana. Bayan ficewar kungiyar daga gasar zakarun Turai da kuma zaman ta a matsayi na 3 yanzu haka a teburin La Liga magoya bayan kungiyar na cigaba da cacakar manaja Ronald Koeman saboda rawar da yake takawa a kungiyar.

Talla

Manajan wanda ya rattaba hannu akan kwangilar shekaru 2 bara na fuskantar matsaloli da suka hada da kokarin lashe kofin La Liga wadda yanzu haka kungiyoyi biyu dake Madrid da suka hada da Real da Atletico ke gaban sa da kuma korar karen da PSG ta musu a gasar Turai.

Karawa tsakanin Barcalona da Athletico Bilbao
Karawa tsakanin Barcalona da Athletico Bilbao CRISTINA QUICLER AFP

Samun nasarar karawar da Barcelona zata yi yau zai taimakawa manaja Koeman amma samun akasi kuma zai dada jefa shakku kan makomar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.