Kwallon Turai

Baraka ta kunno kai a kwallon kafar Turai

Messi da Ronaldo na cikin 'yan wasan da kungiyoyinsu suka shiga cikin sabuwar gasar ta Super League a Turai
Messi da Ronaldo na cikin 'yan wasan da kungiyoyinsu suka shiga cikin sabuwar gasar ta Super League a Turai Josep LAGO AFP

Manyan Kuloblika na gasar firimiyar Ingila  da suka hada da Arsenal da Chelsea da Manchester City da Manchester United da Tottenham sun amince su shiga cikin sabuwar gasar Super League ta Turai duk da gargadin da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya ta yi wa 'yan wasa game da wannan sabuwar gasa.

Talla

Kungiyoyin na Ingila sun bi sahun AC Milan da Atletico Madrid da Barcelona da Inter Milan da Juventus da kuma Real Madrid da suka shiga cikin sabuwar gasar.

Hukumomin sabuwar gasar ta ESL sun ce, wadannan kungiyoyi  da aka assasa gasar da su, sun amince su rika buga gasar a tsakiyar mako,  duk da cewa za su ci gaba da buga wasanninsu na Lig da suka saba bugawa.

ESL ta ce, nan kusa za a fara gudanar da wannan gasa kuma ana sa ran wasu karin kungiyoyi a kalla uku su shigo a dama da su.

Sai dai Firaministan Birtaniya Boris Johnson da kuma mahukuntan Hukumar Kwallon Kafa ta Turai UEFA da Firimiyar Ingila sun caccaki matakin assasa sabuwar gasar.

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta ce, ba za ta amince da wannan gasa ba, kuma duk wanda ya shiga cikinta, to za ta haramta masa buga gasar cin kofin duniya a cewarta.

Hukumomin kwallon kafa na Turai na ganin cewa, sabuwar gasar za ta yi illa ga Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, yayin da ma'assasan sabuwar gasar ke cewa, za ta kawo kudaden shiga fiye da Champions League.

Tuni wasu attajirai da suka hada da manyan kamfanoni da bankuna suka bayyana aniyarsu ta zuba jari a sabuwar gasar saboda kwadayin ribar da za su samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.