Kwallon Kafa

Tottenham ta sallami Mourinho daga aikin kocinta

José Mourinho
José Mourinho Peter Powell Pool/AFP/Archivos

Kungiyar Kwallon Kafar Tottenham Hotspur da ke Ingila ta soke kwangilar manajanta Jose Mourinho saboda abin da ta kira rashin gamsuwa da jagorancinsa watanni 17 bayan hayar sa da ta yi.

Talla

Wannan ya biyo bayan korar kungiyar daga Gasar Cin Kofin Europa da kuma rashin tabuka abin kirkin da take yi a gasar firimiya wanda ya nuna cewar a cikin wasanni 3 da ta buga maki guda kacal ta samu, matakin da ke yi wa kungiyar barazanar samun gurbi cikin manyan kungiyoyi 4 da ke sahun gaba wadanda ake sa ran su samu gurbin karawa a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai ta kaka mai zuwa.

Yanzu haka Tottenham na matsayi na 7 da ke nuna cewar, akwai tazarar maki 5 tsakaninta da kungiyar West Ham da ke matsayi na 4.

Kungiyar ta ce, wadannan rashin nasarorin da kungiyar ta samu sun tilasta mata sallamar Mourinho da daukacin jami’an da ke taimaka masa.

Tettenham ta nada kocin yaran da ke koyan kwallo a kungiyar Ryan Mason a matsayin manajan riko domin shirya ‘yan wasan da za su kara da Southampton ranar Laraba da kuma wasan karshe na cin kofin League Cup da zai gudana a karshen mako.

Daga cikin nasarorin da Mourinho ya samu a kakar bana har da doke tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United da ci 5-1 a gasar firimiya, kungiyar da Tottenham za ta sake karawa da ita a wasan karshe na Carabao ranar 25 ga wannan wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.