Wasanni-Kwallon Kafa

Kungiyoyi 9 cikin 12 sun janye daga gasar Super League

Zuwa yanzu kungiyoyi 9 daga cikin 12 ne suka janye daga matakin mara baya ga gasar ta European super league.
Zuwa yanzu kungiyoyi 9 daga cikin 12 ne suka janye daga matakin mara baya ga gasar ta European super league. REUTERS - DADO RUVIC

Kungiyoyi 9 daga cikin sauran kungiyoyin 12 sun sanar da janyewa daga gasar European Super League da a baya suka amince bayan tsanantar korafe korafe daga magoya baya da kuma barazanar UEFA.

Talla

Kungiyoyin Firimiya 6 da suka kunshi Arsenal da Chelsea da Liverpool da Tottenham baya ga Manchester United da Mancehster City tun a jiya suka sanar da janyewa daga tayin gasar yayinda a safiyar yau litinin sauran kungiyoyin da suka kunshi wasu daga Italiya da kuma Spain suka mara musu baya.

Yanzu haka dai kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid a Spain da Juventus baya ga Inter Milan da AC Milan daga Italiya dukkaninsu sun fitar da sanarwar janyewa daga gasar.

Sai dai kawo yanzu manyan kungiyoyin Spain biyu da suka kunshi Real Madrid da Barcelona ba su ce komai kan matakinsu na goyon bayan gasar ta ESL ba.

Jaridun wasanni sun ruwaito shugaban kungiyar Juventus Andrea Agnelli na cewa tun bayan ficewar kungiyoyin firimiya 6 ya samu yakinin cewa sabuwar gasar ta ESL ba za ta kai labari ba.

Agnelli wanda ke goyon bayan yiwuwar gasar ta ESL yanzu haka na fuskantar takun saka da shugaban hukumar UEFA Aleksander Ceferin bayan matakin ajje mukaminsa na shugabancin hadakar kungiyoyin Turai a Lahadin da ta gabata, yayinda kuma ya ki amfa kiran da kungiyar ke masa ta wayar salula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.