Wasanni-Kwallon Kafa

Kungiyoyin Ingila sun janye daga gasar Super League

An gudanar da zanga-zangar adawa da kafa sabuwar gasar ta Super League
An gudanar da zanga-zangar adawa da kafa sabuwar gasar ta Super League Justin Tallis AFP

Daukacin kungiyoyi 6 masu buga firimiyar Ingila sun janye aniyarsu ta shiga sabuwar gasar Super League ta Turai.

Talla

Manchester City ce ta fara ficewa bayan Chelsea ta nuna alamar janyewa daga cikin wannan gasa mai cike da cece-kuce.

Sauran kungiyoyin na Ingila sun hada da Arsenal da Liverpool da Manchester United da Tottenham da suka bi sahun Manchester City da Chelsea wajen ficewa.

Yanzu haka mahukuntan gasar ta Super League sun ce za su yi nazari kan hanya mafi dacewa domin fasalta gasar.

Wannan na zuwa ne bayan Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta yi gargadin cewa, kungiyoyin da suka shiga cikin gasar za su fuskanci hukunci, yayin da ita ma Hukumar Kwallon Kafa ta Turai  UEFA ta ce, za ta haramta musu buga gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Kodayake wata kotu a birnin Madrid na Spain ta gargadi FIFA da UEFA dangane da yunkurin haifar da tarnaki ga wannan sabuwar gasa wadda ta rarraba kawunan masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa a Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.