Wasanni-Kwallon Kafa

Shugaban Liverpool ya nemi afuwar magoya baya kan Super League

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Liverpool John W Henry.
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Liverpool John W Henry. Oli SCARFF AFP/File

Mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool John W Henry ya nemi yafiyar magoya bayan kungiyar kan abin da ya kira kuskuren amincewa da tayin gasar European Super League ko kuma ESL.

Talla

Kalaman Henry na zuwa ne dai dai lokacin da kungiyoyin Firimiya 6 da a farko suka amince da tayin gasar ta ESL suka janye a yammacin jiya Talata.

Cikin kalaman neman yafiyar na Henry wanda tuni magoya baya suka mayar da martanin cewa ya yi kadan tare da bayyana shi da dadin baki, shugaban ya ce ko shakka babu ya baiwa magoya baya da ‘yan wasan tawagar kungiya wajen amincewa da gasar.

Gabanin kalaman na Henry, ‘yan wasan Liverpool da dama ne suka bayyana rashin goyon bayansu ga gasar ta ESL ciki har da kyaftin Jordan Henderson tare da mataimakinsa James Milner.

Ilahirin kungiyoyin da suka kunshi ita kanta Liverpool da Manchester City da Manchester United da Chelsea da Arsenal da kuma Tottenham sun sanar da janyewa daga gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.