Damben Boxing

Joshua da Fury za su fafata a Saudi Arabiya

Tyson Fury (hagu) da abokin karawar sa dan kasar Burtaniya Joshua sun amince su fafata
Tyson Fury (hagu) da abokin karawar sa dan kasar Burtaniya Joshua sun amince su fafata RINGO CHIU, FAYEZ NURELDINE AFP/File

Kasar Saudiya zata karbi bakwancin karawar da fitattun ‘yan Damben Boxim biyu na ajin nauyi Anthony Joshua da Tyson Fury za su yi, kamar yadda manajan Fury Bob Arum ya tabbatar.

Talla

Dama tattaunawa tayi nisa game neman inda za’ayi da gwabzawar mai dimbin tarihi da aka dade ana jira tun bayan da fitattun biyu suka amince zasu kece raini tsakaninsu.

Da farko dai an gabatar wa ‘yan damben kasashe  irinsu Qatar da Uzbekistan da Rasha da Amurka da kuma Burtaniya, kafin Arum, ya tabbatar da za a yi karawar a Saudiya, wanda ta karbi bakuncin wasan da Joshua ya nasara a karawar da yayi da Anthony Ruiz Jr a shekarar 2019.

Arum ya ce anasaran fafatawar da magoya bayan  Josua da Fury suka dade suna jira a garin Jeddah, tsakanin ko 24 ga watan Yuli  ko 31 ga watan, ko kuma 7 ga watan Agusta mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.