Wasanni-Kwallon Kafa

Modric ya sanya hannu a sabon kwantiragi da Real Madrid

Dan wasan tsakiya na Real Madrid, Luca Modric.
Dan wasan tsakiya na Real Madrid, Luca Modric. © AFP

Dan wasan tsakiya, Luca Modric  ya sanya hannu a wani sabon kwantiragi da kungiyar Real Madrid, kamar yadda shugaban kungiyar, Florentino Perez ya bayyana a yau Alhamis.

Talla

Perez bai yi wani karin bayani a game da kwantiragin da dan shekara 35 din dan kasar Croatia, wanda ya koma kungiyar daga Tottenham a shekarar 2012 ya sanya wa hannu ba.

Ya ce kungiyar ba ta kai ga cimma yarjejeniya da dan wasan baya, Sergio Ramos ba, amma yana fatan kaftin din kungiyar zai ci gaba da zama a Bernabeu.

Perez ya ce ci gaba da kasancewar Ramos a kungiyar ya ta’allaka ne ga nauyin aljihunta, duba da yadda take asarar kudaden shiga, lamarin da ya sa ba ta da tabbaci a game da makomarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.