Wasanni-Kwallon Kafa

Zidane ya yaba da bajintar da Benzema ke nunawa

Dan wasan gaban Real Madrid, Karim Benzema.
Dan wasan gaban Real Madrid, Karim Benzema. JAVIER SORIANO AFP/Archives

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane  ya jinjina wa   dan wasan gaban kungiyar, Karim Benzema, bayan da dan kasar Faransan ya zura kwallaye biyu a raga a wasan La Liga tsakaninsu da Cadiz, lamarin da ya kai su ga darewa saman teburin gasar.

Talla

Kwallayen da Benzema  ya ci sun sa ya yi kankankan da shahararren dan wasan kungiyar, Raul Gonzalez, wanda ya saka kwallaye a ragogin kungiyoyin La Liga dabam dabam har 35  a yayin zamansa a Spain.

Zidane ya bayyana farin ciki da bajintar da Benzema ke nunawa, yana mai bayyana shi a matsayin dan wasa mai mahimmanci a kungiyar, wanda ba kawai yana cin kwallaye ne ba, yana kuma taimaka wa dimbim ‘yan wasa su na haskawa.

Benzema ya ci kwallon farko a wasan ne ta wajen bugun daga – kai – sai – mai – tsaron – raga, karon farko da Madrid ke samun irin wannan bugun tun a watan Oktoban 2020.

Ya kuma taimaka Alvaro Odriozola ya ci kwallonsa ta farko a babbar gasar La Liga.

Nasarar ta kai Real saman teburin La Liga da maki 70 a gaba da Atletico Madrid, wadanda suka buga wasanni kasa da Real din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.