Olympic-Brazil

Brazil na son PSG ta bai wa Neymar damar doka wasannin Olympic

Dan wasan gaba na Brazil da ke taka leda a PSG.
Dan wasan gaba na Brazil da ke taka leda a PSG. Paolo AGUILAR POOL/AFP

Hukumar kwallon kafar Brazil ta mikawa PSG bukatar baiwa dan wasan gabanta Neymar Junior damar taka leda a wasannin da kasar za ta faffata yayin gasar Olympic a Tokyo.

Talla

A wata zantawar kocin na Brazil da jaridar wasanni ta Globo, ya ce Neymar na daga cikin ‘yan wasansu sahun gaba da su ke fatan su taka leda yayin gasar ta Olympic ganin irin bajintar da ya nuna a makamanciyar gasar cikin shekarar 2016 a Rio de Jannero.

Sai dai shi da kansa da Kocin na Brazil ya ce abu ne mai wuya PSG ta amince da bai wa dan wasan dama la’akari da yadda ya ke shirin taka leda a gasar Copa America tsakanin ranakun 13 ga watan Yuni zuwa 11 ga watan Yuli.

Gasar ta Olympic dai za ta fara ne kwanaki 10 bayan Copa America kuma za a kammala ta ranar 8 ga watan Agusta wato kwanaki 2 bayan bude sabuwar kakar gasar Ligue 1 a Faransa wanda ken una abu ne mai wuya PSG ta baiwa dan wasan dogon hut una tsawon kwanakin.

Karkashin dokokin kungiyoyin Turai dai kowanne Club na da damar hana dan wasan halartar kowacce irin gasa matukar ba FIFA ce ta shirya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.