Wasanni

Kungiyoyin da suka janye daga shirin gasar Super League basu da hurumi - Perez

Shugaban Kungiyar Real Madrid Florentina Perez dake cewa  gasar Super League na nan daram
Shugaban Kungiyar Real Madrid Florentina Perez dake cewa gasar Super League na nan daram FRANCK FIFE AFP/File

Shugaban Kungiyar Real Madrid Florentina Perez yace kungiyoyin nan guda 12 da suka sanya hannu kan shirin fara gasar Super League wadda ta gamu da adawa daga FIFA da UEFA da kuma kungiyar kasashen Turai basu da hurumin janyewa saboda kwangilar da suka sanya hannu akai.

Talla

Wannan ya biyo bayan matakin da 9 daga cikin kungiyoyin 12 suka dauka na janyewa sakamakon mahawara mai zafi da ta fito daga hukumomin kwallon kafar Duniya da Turai da kuma shugabannin wasu kasashen dake yankin.

Perez dake shugabancin gasar wadda ta kunshi makudan kudade yace a hukumance wadannan kungiyoyi sun riga sun rattaba hannu akan kwangila kuma basu da hurumin janyewa.

Matsin lamba ce ta sanya kungiyoyin janyewa

Shugaban kungiyar yace ya fahimci cewar matsin lamba daga bangarori daban daban ne ya tilastawa kungiyoyin janyewa, amma yana da yakinin za’a fara gasar nan bada dadewa ba.

Kungiyoyin da suka janye sun hada da guda 6 dake Ingila dake gasar Firimiya da suka hada da Manchester United da Manchester City da Liverpool da Arsenal da Tottenham da kuma Chelsea.

Sauran wadanda suka janye sun hada da AC Milan da Inter Milan, yayin da kungiyoyin Real Madrid da Barcelona da kuma Juventus suka ki cewa komai akan lamarin.

FIFA da UEFA na adawa da shirin

Gwamnatocin kasashen da kungiyoyin 12 suka fito tare da hukumomin FIFA da UEFA da kuma kungiyar kasashen Turai sun bayyana adawa da wannan yunkuri wanda suka ce ya sabawa kudirorin su, kuma yin hakan zai iya shafar kimar gasar wasannin su dake gudana yanzu haka.

Hukumomin sun bayyana shirin daukar matakai masu karfi kann duk wata kungiyar da ta yadda ta shiga wannan sabuwar gasa, ciki harda hana 'yan wasan ta shiga duk wata gasa da ta shafi na Turai da na duniya.

Katafaren Bankin JP Morgan ya bada gudumawar euro biliyan 3 da rabi domin fara gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.