Wasanni - Gasar Zakarun Turai

Abu ne marar yiwuwa a hana Real Madrid doka gasar zakarun Turai- Zidane

Kocin Real Madrid, Zinédine Zidane, bayan lashe kofin zakarun Turai karo na 13 a tarihin kungiyar.
Kocin Real Madrid, Zinédine Zidane, bayan lashe kofin zakarun Turai karo na 13 a tarihin kungiyar. GENYA SAVILOV AFP/Archives

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinedine Zidane ya ce rashin azanci ne wani ya yi tunanin za a iya dakatar da kungiyar daga shiga gasar cin kofin zakarun Turai.

Talla

Kalaman na Zidane wanda ke zuwa bayan tsanantar kiraye-kiraye wajen ganin UEFA ta zartas da hukuncin dakatarwa kan kungiyoyi 12 da suka amince da tayin Super League, ya ce abu ne da bazai yiwu ba kuma baya bukatar dogon tunani.

Madrid wadda ke tunkarar kofin gasar na 14 a tarihi yayin karawarta da Chelsea a gobe talata, Zidane ya nanata cewa gasar zakarun turai bazata yiwu ba Real Madrid ba.  

Madrid wadda ke jerin kungiyoyin 12 da suka nemi yiwa gasar zakarun turai kishiya, har zuwa yanzu shugabanta Florentino Perez ya kafe kan cewa gasar ta Super League za ta gudana kamar yadda aka tsara.

Perez ya gargadi kungiyoyi 9 da suka fice daga gasar cikin kasa da sa’oi 72 bayan tsannatar boren magoya baya da cewa, basu da hurumin fita daga gasar bayan rattaba hannu kan kwantiragi.

Kungiyoyin da suka fice daga gasar sun kunshi na Firimiya 6 wato Liverpool, Arsenal, Chelsea da Tottenham sai kuma Manchester City da Manchester United kana AC Milan da Inter Milan daga Italiya tukuna Atletico Madrid daga Spain yayinda Barcelona da Real Madrid da kuma Juventus suka ki daukar makamancin matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.