Wasanni-Kwallon Kafa

Chelsea ba ta goyon bayan fadada gasar zakarun Turai- Tuchel

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Thomas Tuchel.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Thomas Tuchel. Ben STANSALL AFP/File

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Thomas Tuchel ya ce tawagarsa bata goyon bayan shirin fadada gasar cin kofin zakarun Turai wanda zai karawa ‘yan wasa yawan wasannin da za su doka karkashin gasar a kowacce kaka.

Talla

Bayan gaza cimma kudirin tabbatuwar gasar European Super League da ta yamutsa hazo cikin duniyar kwallo a baya-bayan nan wadda kungiyoyin Turai 12 suka amince gabanin janyewar 9, UEFA ta amince da fadada gasar ta zakarun Turai.

Sabon zubin gasar wanda zai kunshi kungiyoyin Turai 36 sabanin 32 ya nuna cewa kungiyoyin gasar za su samu karin akalla wasanni hur-hudu akan yadda suka saba.

A zantawarsa gabanin wasan Chelsea da Real Madrid karkashin gasar ta zakarun turai a gobe Talata, Tuchel ya ce bashi da tabbacin ko gasar ta iya kayatar da masu kallo amma har zuwa yanzu yana ganin zubin na tattare da kura kurai la’akari da yadda ‘yan kallo za su wahalta matuka.

A cewar kocin na Chelsea tashin hankalin yakar gasar Super League ya mantar da su ta’asar da aka yiwa gasar ta zakarun Turai da ke bukatar sanya bakin kungiyoyi don kalubalantar matakin UEFA.

Kafin Tuchel dai, daidaikun ‘yan wasa da dama ne suka fara korafi kan matakin na UEFA dangane da fadada gasar ta zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.