Inter Milan ta lashe gasar Seria A karo na farko tun shekarar 2010
Wallafawa ranar:
Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta yi nasarar lashe gasar Serie A karo na farko tun daga shekarar 2010 sakamakon kunnen dokin da kungiyar Atalanta wadda ke bin ta a teburin gasar na Italia ta yi da kungiyar Sassuolo.
Inter wadda ta doke kungiyar Crotone a ranar Asabar ta haramtawa kungiyar Juventus kare kambin da ta samu a shekarar da ta gabata da kuma lashe kofin a karo na 10 a jere.
Juventus ta rasa dama
Shugaban kungiyar Juventus Andrea Agnelli ya aike da sakon taya murna ga takwaran sa na Inter Steven Zhang sakamakon wannan gagarumar nasarar da suka samu.
Daga cikin 'Yan wasan da suka taka gagarumar rawa wajen nasarar kungiyar Inter Milan akwai Romelu Lukaku mai shekaru 27 da aka sayo euro miliyan 80 daga Manchester United wanda ya zirara kwallaye 27, sai Nicolo Barella mai shekaru 24.
Sauran sun hada da Acraf Hakimi da Matteo Darmian da Christian Eriksen da aka sayo daga Tottenham Hotspur.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu