La liga

Barcelona ta samu karin maki 3 dakyar bayan doke Valencia da ci 3 -2

Messi yayin bugun tazara da ya bashi damar zura kwallo na biyu a wasan da suka ci Valencia ci 3-2 a gasar La Liga 2 ga watan Mayu 2021
Messi yayin bugun tazara da ya bashi damar zura kwallo na biyu a wasan da suka ci Valencia ci 3-2 a gasar La Liga 2 ga watan Mayu 2021 JOSE JORDAN AFP

Barcelona ta samu maki uku dakyar a fafatawar da ta doke Valenci da ci 3-2  a waje a wasan mako na 34 na gasar Laligar Spain.

Talla

Kungiyoyin biyu sun fafata mintuna 45 ba tare da zura kwallo a raga ba, har sai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci da mintuna biyar Valencia ta fara zura kwallo a ragar Barcelona ta hannun Gabriel Paulista.

Lionel Messi da Antoine Griezmann na murnar cin kwallo
Lionel Messi da Antoine Griezmann na murnar cin kwallo JOSE JORDAN AFP

Kafin Lionel Messi ya farke wa Barcelona bayan mintuna bakwai da kwallon farko, sai Antoine Griezmann ya kara na biyu daga baya kyaftin din Argentina ya ci na uku, wato na biyu a wasan, duk da barar da finareti da ya yi.

Kafin tashi daga wasan Valencia ta ci kwallo na biyu, aka tashi wasa Barcelona 3 – Valencia 2.

Messi yayin fafatawa da Valencia a gasar La Liga  2 ga watan Myau 2021
Messi yayin fafatawa da Valencia a gasar La Liga 2 ga watan Myau 2021 JOSE JORDAN AFP

Har yanzu Atletico Madrid ke jan ragamar Lilaga ta Bana da maki 76, Barcelona dake ta uku tana da maki daya da abokiyar hamayyarta Real Madrid dake na biyu a teburin da maki 74 -74 ko wannensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI