Wasanni - EPL

Tottenham ta kama hanyar cika burinta na samun gurbi a gasar zakarun Turai

Dan wasan Totteham Gareth Bale yayin wasa a gasar Premier Ingila
Dan wasan Totteham Gareth Bale yayin wasa a gasar Premier Ingila Martin Rickett POOL/AFP

Tottenham ta kama hanyar cika burinta na samun gurbi a gasar neman cin kofin zakarun Turai a badi, sakamakon nasarar doke Sheffield United da ci 4-0 a wasan mako na 34 na gasar Premier Ingila da suka fafata jiya.

Talla

Gareth Bale kadai ya zura kwallaye uku cikin hudu da kungiyar tayi nasara da su kan Sheffield United.

Gareth Bale na murnar lashe kwallo yayin wasansu da Burnley
Gareth Bale na murnar lashe kwallo yayin wasansu da Burnley DANIEL LEAL-OLIVAS POOL/AFP

Da wannan sakamakon Tottenham na mataki na biyar a teburin gasar EPL da tazarar maki biyar tsakaninta da ta Chelsea dake ta hudu.

'Yan wasan Tottenham yayin murnar zura kwallo
'Yan wasan Tottenham yayin murnar zura kwallo Andy Rain POOL/AFP

Man City ke jan ragamar Teburin da maki 80, sai Man United a matsayin na biyu da maki 67 sai kuma Leister city a matsayi na uku, amma har yanzu saura wasanni hudu kafin karkare kakar bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.