Wasanni - Gasar Zakarun Turai

Mbappe zai iya rasa karawar PSG da Manchester City a gasar zakarun Turai

Kylian Mbappe yayin wasan PSG da tsohon Club dinsa Monaco.
Kylian Mbappe yayin wasan PSG da tsohon Club dinsa Monaco. FRANCK FIFE AFP

Babu tabbacin ko Kylian Mbappe zai taka leda a karawar PSG ta Faransa da Manchester City karkashin gasar cin kofin zakarun Turai a haduwa ta biyu da kungiyoyin za su yi yau talata a rukunin wasan gab da na karshe.

Talla

Mbappe mai shekaru 22 bai samu damar taka leda a karawar da PSG ta yi nasara kan Lens a asabar din nan ba, saboda raunin da ya ke fama da shi a kafa.

Mai horar da kungiyar ta PSG Mauricio Pochettino ya ce Mbappe ya fara atisaye daga jiya litinin sai dai likitoci ba su tabbatar da cikakiyar lafiyarsa da za ta kai ga taka leda a wasan na yau ba.

Cikin wannan kaka kadai, Mbappe ya zura kwallaye 37 a wasanni 43 ciki har da 10 da ya zura a wasannin gasar ta cin kofin zakarun Turai.

A haduwar farko tsakanin PSG da Cityn dai wasan da ya gudana a Paris, Cityn ce ta yi nasara da kwallaye 2 da 1.

A bangare guda Neymar Junior ya yi ikirarin cewa zai yi dukkan mai yiwuwa wajen bayar da gudunmawar ganin tawagarsa ta doke City ko da zai rasa ransa a filin was.

Neymar a zantawarsa da jaridun wasanni a faransa ya ce yana da kwarin gwiwar tawagar ta sa za ta kai wasan karshe tare da dage kofin a bana, duk da gagarumin aikin da ke gabansu ganin yadda City ta yi nasara kansu har gida.

Ko a kakar da ta gabata PSG ta yi nasarar kai wa wasan karshe amma kuma ta yi rashin nasara hannun Bayern Munich.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI