Wasanni-Kwallon Kafa

Tuchel zai yi amfani da salo wajen hana Real Madrid nasara a haduwarsu

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Thomas Tuchel tare da wasu 'yan wasansa.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Thomas Tuchel tare da wasu 'yan wasansa. JAVIER SORIANO AFP

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thomas Tuchel na shirin amfani da wani salo a karawarsu da Real Madrid don kange kyaftin din tawagar Sergio Ramos ba kuma tare da hada shi da wani dan wasa ba.

Talla

Tuchel wanda ya kware wajen sanya lamba tarar bogi a fili don karkatar da hankalin masu tsaron baya musamman a wasannin baya-bayan nan, ana ganin zai yi amfani da makamancin salon don raba hankalin masu tsaron bayan na Madrid, dai dai lokacin da Chelsea ke fatan kai labari a karawar bayan tashi wasa 1 da 1 a haduwarsu ta farko a Spain.

A sakon da ya wallafa a shafinsa, Tuchel ya bayyana yadda ya ke yawan amfani da dan wasa Kai Havart wajen buga lamba 9 amma na bogi, wanda kuma ya na aiki matuka wajen karkatar da hankalin masu tsaron bayan.

Ramos wanda ya yi fama da jinyar da ta tilasta masa rasa haduwar farko, a wannan karon ne zai dawo wasa kuma ana ganin zai yi dukkan mai yiwuwa wajen taimakawa tawagar tasa ta hanyar kange ratata mata kwallaye.

Chelsea dai na kan ganiyarta ne a wannan kaka la'akari da irin nasarorin da ta ke samu a gasar Firimiyar Ingila, ko da Real Madrid ta yi kaurin suna wajen bayar da mamaki a gasar cin kofin zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.