Wasanni

Argentina na bukatan kulla alakar wasanni da Najeriya

Leonel Messi yayin fafatawar Argentina da Najeriya
Leonel Messi yayin fafatawar Argentina da Najeriya REUTERS/Sergio Perez

Jakadan Argentina a Najeriya, Alejandro Herrero ya bukaci karfafa alakar kwallon kafa tsakanin kasarsa da Najeriya.

Talla

Herero ya mika wannan bukatar ce, yayin ganawa da Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Najeriya kuma memba a Majalisar FIFA, Amaju Pinnick, inda yace, ya lura cewa akwai abubuwa masu kamanceceniya  tsakanin kasashen biyu a wasan kwallon kafa.

Jakadan ya kuma yi tuni da lokuta da dama na fafatwa tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa “Najeriya da Argentina a koyaushe suna fafatawa a gasar cin kofin duniya ta FIFA, kuma ko da za’a doke Najeriya to babu tazarara sosai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.