Wasanni - Gasar Zakarun Turai

Chelsea da Manchester City za su hadu a wasan karshe na zakarun Turai

Manchester City da Chelsea za su hadu da juna a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai.
Manchester City da Chelsea za su hadu da juna a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai. Adam Davy POOL/AFP/File

Kungiyoyin kwallon kafa na Manchester City da Chelsea za su hadu da juna a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai da zai gudana ranar 29 ga watan nan a Istanbul, bayan nasararsu ta doke PSG da Real Madrid.

Talla

A daren jiya ne Chelsea ta yi nasarar yin waje da Real Madrid daga gasar bayan zura mata kwallaye 2 da nema kari kan guda da ta zura mata a gidanta tun haduwarsu ta farko wadda aka tashi wasa daya da daya.

A bangare guda ita ma Manchester City ta yi nasarar kai wa wasan karshen ne bayan lallasa PSG ta Faransa da kwallaye 2 da nema.

Wasan karshen dai zai zama kamar yadda ya gudana a 2019 lokacin da kungiyoyin firimiya na Liverpool da Tottenham suka hadu da juna, inda Liverpool ta yi nasarar doke Tottenham.

Tsakanin kungiyoyin biyu na City da Chelsea kowacce na ji da bajinta a wannan karon, bayan da kowacce ke ci gaba da nuna rawar gani a wannan kaka, inda City ke jagoranci teburin Firimiya yayinda Chelsea ke matsayin ta 4.

Mai horar da kungiyar Manchester City dai ya yi ikirarin cewa rashin lashe kofin zai zame masa tamkar koma baya a tarihin horarwarsa yayinda takwaransa na Chelsea Thomas Tuchel ke cewa lokaci ya yi da za su nuna City iyakarta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI